Praministan Birtaniya ya kare matsayinsa game da Euro

Praministan Birtaniya David Cameron Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Praministan Birtaniya David Cameron

Praministan Birtaniya, David Cameron, da kuma mataimakinsa Nick Clegg, sun kara fito da irin bambance bambancen dake tsakaninsu a fili, kan yadda Birtaniya ta ki amincewa da matakan da Tarayyar Turai ta yi kokarin dauka, na ceto kudin Euro a makon da ya wuce.

A lokacin da yake jawabi a majalisar dokokin Birtaniyar, Mr Cameron ya ce ba a baiwa kasar tasa isasshen tabbaci na kare cibiyoyin kudinta ba.

Mr Clegg, jagoran 'yan jam'iyyar Liberal a gwamnatin kawancen bai halarci zaman muhawarar ba.

Amma ya shaidawa manema labaru cewa ba ya goyon bayan Mr Cameron.

Shi kuma Ed Miliband, jagoran jam'iyyar adawa ta Labour a majalisar, ya zargi Mr Cameron da dawowa hannu rabbana daga taron na Brussels, a maimakon ya tsaya ya kare matsayinsa.

Karin bayani