Baraka a jamiyyar PDP ta Sokoto

taswirar Nigeria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption taswirar Nigeria

Wata baraka ta kunno kai a jam'iyyar PDP mai mulkin jahar Sakkwato dake arewacin Najeriya inda wani bangare na shugabannin zartarwar ta, suka sanar da rushe shugabancin jam'iyyar na jahar tare da nada wani sabo.

Shugabancin jam'iyyar da aka ce an rusa dake karkashin jagorancin Alhaji Tukur Waziri yayi watsi da matakin rusa su, kuma suka ce suna nan daram a kan mukamansu.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar ke shirin gudanar da zaben fitar da dan takarar gwamna a karshen makon nan.