Vladimir Putin zai fuskanci babban kalubale

Vladimir Putin na Rasha Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Vladimir Putin na Rasha

Wani hamshakin attajiri dan kasar Rasha , Mikhail Prokhorov, ya ce zai kalubalanci Vladimir Putin a zaben shugaban kasar da za a gudanar cikin watan Maris mai zuwa.

Mr Prokhorov ya ce irin zanga zangar nunan kin jinin gwamnatin da aka rika gudanarwa a 'yan kwanakin nan, wadda a baya ba a taba ganin irin ta ba, alama ce dake nuna cewa al'ummar Rasha ta fara farkawa daga barci.

Wakilin BBC a Mosko ya ce akwai matukar rashin amincewa da manyan attajiran kasar Rasha, don haka babu tabbas kan irin goyon bayan da zai samu.

Karin bayani