Ana gudanar da zabe a Syria

zaben syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption zanga zangar a syria

Ana gudanar da zaben kananan hukumomia Syria, duk da tashin hankalin da ke kara muni tsakanin jami'an tsaro da masu zanga zangar nuna kyamar gwamnati.

Zanga zagar dai ta yi sanadiyar mutuwar dubban mutane.

Gwamnatin Syriar ta ce zaben na daga cikin irin sauye-sauyen da take son bullowa da su, a sakamakon zanga zangar.

Su dai 'yan adawa sun yi watsi da matakin, suka kuma bukaci jama'a da su kaurace ma zaben. Ba a sa ran jama'a da dama zasu fito zaben, ta wani bangaren saboda kauracewar, ko kuma a sakamakon fargaba kan harkokin tsaro.