Wani matashi ya kai hari a Belgium

Harin da aka kai a Liege na kasar Belgium Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Harin da aka kai a Liege na kasar Belgium

Wani mutum ya bude wuta da bindiga, kana ya jefa nakiyoyi daga rufin wani gini, inda ya halaka mutane uku kafin ya kashe kansa, a wata kasuwa dake cike da masu sayayyar kirsimati, a birnin Liege na kasar Belgium.

Akwai wasu mutanen su saba'in da biyar da suka jikkata, wasu daga ciki munanan raunuka.

Yansanda sunce, suna daf da yiwa maharin tambayoyi kafin hawa kan rufin wani gini a tsakiyar Liege.

Daga nan kuma sai ya jefa gurneti sannan ya yi harbi kan taron jama'a a Kasuwa, kafin ya kashe kansa.

Mai gabatar ka kara ta birnin Liege, Daniele Reynders ta ce wanda ya kai harin, ana kiransa Nurudin Amrani, da aka haifa ranar 15 ga watan Nuwamban 1978. Kuma shi kadai ya kai harin.

Karin bayani