Canada ta janye daga yarjejeniyar Kyoto

Mnistan muhalli na Canada, Peter Kent
Image caption Mnistan muhalli na Canada, Peter Kent

Canada ta zama kasa ta farko da ta janye a hukumance daga yarjejeniyar rage fitar da iska mai guba ta Kyoto.

Ministan muhallin kasar, Peter Kent ya ce, yarjejeniyar ba za ta samar da mafita ba ga kasar game da matsalolin muhalli.

Sanarwar janyewar ta zo ne kwana guda bayan an kammala taron kasa-da-kasa a kan sauyin yanayi a Durban, wanda aka kammala ba tare da an cimma matsaya a kan yarjejeniyar da za ta maye gurbin ta Kyoton ba.

Yarjeniyar Kyoto za ta daina aiki a karshen shekara mai zuwa.

Sai dai 'yan adawa sun soki matakin gwamnatin kasar, inda suka ce ta zuzuta irin kudaden da kasar ke kashewa wurin ci gaba da kasancewa a cikin yarjejeniyar ta Kyoto, ba tare da yin la'akari da nauyin da ya rataya a wuyanta na rage hayaki mai guban ba.