An yi sabuwar mai gabatar da kara ta ICC

Sabuwar mai shigar da kara a ICC, Fatou Bensouda Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sabuwar mai shigar da kara a ICC, Fatou Bensouda

Kasashe mambobin kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, sun zabi wata lauya yar Gambia, Fatou Bensouda a matsayin sabuwar babbar mai shigar da kara ta kotun.

Kasashen sun amince da zaben na ta ne, a lokacin wani taron da Majalisar dinkin duniya ta yi a birnin New York.

Ms. Bensouda ta ce za ta ci gaba da tabbatar da cewa masu aikata laifi sun fuskanci hukunci ko da kuwa daga wacce kasa suka fito.

Sai dai masu sharhi kan al'amuran yau da kullum sun bayyana cewa, da wuya ta sauya zani game da yadda kotun ke gudanar da ayyukanta.