Jonathan ya gabatar da kasafin kudin 2012

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya gabatar da kasafin kudin kasar na shekarar 2012 ga majalisun dokokin kasar wanda adadinsa ya kai kusan naira tiriliyan 5 wato (dala biliyan 29.30).

Jonathan ya ce gwamnati za ta kara kashe kudade idan aka kwatanta da kasafin kudin na bana wanda adadinsa ya kai naira tiriliyan 4.48.

Amma ya ce adadin kudaden da ake kashewa wajen tafiyar da ayyukan gwamnati ya ragu daga kashi 74 cikin dari zuwa kashi 72 inda gwamnati za ta mayar da hankali wajen ayyukan gina kasa.

"Wannan kasafin kudin wani mataki ne a kokarin da muke yi na bunkasa tattalin arzikin kasarmu...ba za mu jefa rayuwar 'yan Najeriya cikin hatsari ba; dole ne mu kare kanmu ta hanyar yin taka-tsan-tsan wajen tsara yadda za mu ringa kashe kudade," a cewar Jonathan.

Masana sun yi tsokaci

Za a rage gibin kasafin kudin da kashi 2.77 cikin dari daga kashi 2.96 idan aka kwatanta da kasafin bana, kamar yadda Jonathan ya shaida wa 'yan Majalisar.

Ya kara da cewa an tsara kasafin kudin na 2012 ne kan dala 70 a kan kowacce gangar danyan mai, da kuma hako ganga miliyan 2.48 ta danyar man a kowacce rana.

Amma masana na ganin kara adadin kudin da za a kashe hatsari ne a wannan lokacin da ake fama da koma-bayan tattalin arziki a duniya.

"Ya kamata a ce akwai kariya domin fuskantar irin kalubalen da ka iya fuskantar fannin mai na kasar," kamar yadda Razia Khan, na sashen binciken Afurka a Standard Chartered, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

An tsara kasafin kudin na 2012 a kan musayar naira 155 ga dala daya, da kuma hauhawar farashi a kan kashi 9 da rabi cikin dari.

A yanzu dai akwai matukar hauhawar farashi, kuma ana musayar naira ne kan 160 ga dalar Amurka daya.

Karin bayani