Goodluck zai gabatar da kasafin kudi

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

A yau ne shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan zai gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa ga majalisar dokokin kasar.

Sai dai masana a fannin tattalin arziki na korafin cewa ba'a aiwatar da kasafin kudi dari-bisa dari a baya, ta yadda zaiyi tasiri sosai.

Gabatar da kasafin kudin na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da cece kuce kan maganar janye tallafin mai fetur.

Tuni aka samu rarrabuwar kawuna tsakanin 'yan majalisar, inda wasu ke goyon bayan shirin gwamnati na janye tallafin, yayin da wasu kuma ke adawa da shirin.