An yi nasara a yaki da zazzabin cizon sauro

Yaki da zazzabin cizon sauro Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Yaki da zazzabin cizon sauro

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce an samu ci gaba a yaki da zazzabin cizon sauro, amma akwai bukatar kara zuba kudade , idan ana son cinma buri da ake so na kawar da mace mace a sakamakon cutar nan da shekara ta 2015.

Wakiliyar BBC ta ce, Hukumar ta WHO ta ce mutane sama da dubu dari shidda da hamsin ne suka mutu a sakamakon zazzabin malaria a 2010, kuma galibinsu kananan yara ne 'yan Afrika.

Adadin wadanda suka rasun ya ragu da kashi biyar cikin dari, in aka kwatanta da shekarar da ta gabace ta.

Hukumar ta WHO ta ce hakan na nuna cewar ana samun ci gaba, amma duk da haka adadin wadanda suka mutun yana da yawa, daga cutar da za a iya magance ta.

Karin bayani