An shiga zagaye na biyu na zaben yan majalisar Masar

zaben Masar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption zaben Masar

Masu zabe a kasar Masar sun koma rumfunan zabe a yau Laraba, inda za su kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokokin kasar a zagaye na biyu wanda aka dade ana jira.

Jam'iyyun masu ra'ayin addinin Islama na sa ran sake samun nasara, yayin da zaben ke kaiwa ga yankunan karkara.

To sai dai da alamu zaben na neman zamantowa tamkar fagen daga ne ga kungiyoyin da ke da bambancin ra'ayi a kan irin rawar da ya kamata addinin Islama ta taka a harkar siyasa.

Yan takara a jamiyyun masu raayin yanci, ba su tabuka wani abin kirki ba a zaben, inda suke a matsayi na ukku.

Banbancin dake tsakanin jamiyyar yan uwa musulmi da yan Salafiyyun na da muhimmanci, domin yan uwa musulmin sun nuna kansu a matsayin masu matsakaicin raayi. To amma a bangare guda yan Salafiyyun ba su da wani sassauci, saidai kuma suna da alaka da talakawan kasar Misra.