Al-Maliki na zawarcin yan kasuwar Amurka

PMn Iraqi al-Maliki Hakkin mallakar hoto 1
Image caption PMn Iraqi al-Maliki

PMn Iraqi Nuri al-Malaki, yayi kira ga kamfanonin Amurka da su sanya jarinsu a kasarsa, yayinda dakarun Amurka ke shirin ficyewa daga Iraqi.

A lokacinda yake jawabi ga manyan yan kasuwa a Washington, Mr al-Maliki ya ce, makomar Iraqi za ta kasance ne a hannun manyan kamfanoni maimakon hannun hafsoshin soji.

Ya kara da cewa, alfanun da kamfanonin Amurka za su samu ba zai misaltu ba a kasar dake kokarin sake ginuwa, bayan yaki ya daidaita ta.

To saidai har yanzu akwai damuwa dangane da yanayin rashin tabbas na tsaro a kasar, wanda ya kan sanya a kasa bin kaida a maaikatu da dama.

Dakarun Amurka na karshe dai, watakila za su bar kasar ne a karshen wannan shekara.