Jamiyya mai mulkin Ivory Coast na kan gaba

zaben Ivory Coast Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption zaben Ivory Coast

Yanzu haka dai an fara samun sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin da aka yi ranar Lahadi a Ivory Coast.

Sakamakon da ya samu kuma ya nuna cewa jam'iyya mai mulki ta RDP ce ke da rinyayen kuri'u.

Jam'iyyar tsohon shugaba Laurent Gabgbo dai ta kauracewa zaben.

Masu sharhin kan alamrun yau da kullum sun ce da wuya zaben ya taimaka wajen hada kan 'yan kasar ta Ivory Coast.

Saidai akwai wadanda ke ganin cewa, zaben wata matashiya ce ta farfado da tattalin arzikin kasar, wanda a karshe zai hada kan yan kasar.