Barazana daga kungiyar AQMI

Malam Bazoum Mohammed Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Malam Bazoum Mohammed

Gwamnatin Jumhuriyar Nijar ta ce tana daukan kwararan matakai na tunkarar barazanar da kasar ke fuskanta daga kungiyar al Qaida a yankin Maghrib, watau AQMI.

Yanzu dai gwamnatin Nijar din ta ce ta baiwa sojojinta dake aikin kare iyakokin kasar, karin kayan aiki na zamani.

Ministan harkokin wajen Nijar, Malam Bazoum Mohammed ne ya furta hakan a lokacin ziyarar da ya kawo mana nan London.

Mr Bazoum ya ce kasashe masu hannu da shuni sun kudiri anniyar taimaka wa kasashen yankin Sahel a yakin da suke yi da kungiyar ta AQMI.

A makon jiya ma, ministocin harkokin wajen kasashen Nijar da Mali da Mauritania suka gaana da Babbar jami'ar Tarayyar Turai mai kula da manufar harkokin waje, Catherine Ashton, inda suka tattauna a kan wannan batu.

Yanzu haka dai, wasu baki 9 ne da suka hada da Faransawa 5, kungiyar ta AQMI da wasu kungiyoyin daban ke rike da su, bayan da suka yi garkuwa da su a kwanan baya.

Karin bayani