Sojojin Amurka na karshe a Iraki na komawa gida

Shugaba Obama Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Obama

Shugaba Obama ya yi marhabin ga wasu daga cikin dakarun Amurka na karshe dake komawa gida daga Iraki, lamarin dake kawo karshen kusan shekaru tara da Amurka ta kwashe tana yaki a kasar.

Lokacin da yake jawabi a Fort Bragg, a jihar North Carolina Mr Obama ya bayyana lokacin da cewa mai cike da tarihi ne.

Shugaba Obama ya ce sadaukar da kan da sojojin suka yi, ya samar da sabuwar Iraki mai 'yanci.

Wani wakilin BBC a Washington ya ce shugaba Obama na cika alkawarin da ya dauka ne lokacin yakin neman zabe, cewa zai dawo da sojojin kasar gida daga Iraki, in ya lashe zaben.

Karin bayani