Juyin Juya halin kasashen Larabawa, alheri ne.

Binciken BBC
Image caption Binciken BBC

Wani sabon binciken jin ra'ayoyin jama'a da BBC ta gudanar a kasashe 22 ya nuna cewa kusan mafi yawan mutanen da aka yiwa tambayoyi sun ce, tarzomar da ta haifar da sauyi a wasu kasashen larabawa aba ce mai kyau.

Kashi hamsin da biyar daga cikin wadanda aka yi wa tambayoyi game da zanga zangar kasashen Larabawa ne suka nuna cewa aba ce mai kyau.

To saidai kashi 22 cikin dari sun nuna cewa zanga zangar ba alheri ba ne.

Raayin mutane a kasar Russia ya fita zakka, inda mafi akasarin wadanda aka yi wa tambayoyi game da batun, sun nuna cewa zanga zangar kasashen Larabawa ba abu ne mai alheri ba.