Iraki za ta fuskanci jarrabawa- Panetta

Leon Panetta Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Leon Panetta

Sakataren tsaron Amurka, Leon Panetta ya ce kasar Iraki za ta fuskanci jarrabawa a cikin kwanakin da ke tafe daga mutanen da ke son raba kan kasar.

Sakataren tsaron ya yi jawabi ne a wajen bikin da ya kawo karshen yakin da sojojin Amurka ke yi a kasar Iraki, inda ya ce kalubalen da Irakin za ta fuskanta sun hada da ta`addanci da bukatar kafa demokuradiyya.

Amma ya yi alkawarin cewa kasarsa za ta ci gaba da tallafa wa kasar Irakin.

Ragowar Sojojin Amurkan da suka kai dubu hudu za su fice daga kasar ne cikin `yan kwanaki masu zuwa, koda yake wasu masu horar da sojoji da wasu `yan kwangila daga cikinsu za su ci gaba da kasancewa a kasar.

Karin bayani