Bincike kan daukan hoton gidan Mandela

Gidan Nelson Mandela dake garin Qunu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gidan Nelson Mandela dake garin Qunu

Rundunar `yan sanda kasar Afirka ta kudu ta ce ta fara gudanar da bincike a kan wasu kamfanonin yada labarai biyu da take zargin sun dauki hotunan bidiyo na gidan da tsohon shugaban kasar Nelson Mandela ke da zama.

Rundunar `yan sandan dai na zargin cewa kemarorin da aka yi amfani da su na kamfanonin dillancin labaran Reuters da Associated Press ne. Amma Kakakin kamfanin Associated Press ya musanta zargin.

Kakakin rundunar `yan sandan kasar Afirka ta kudu, Kanar Visnu Naidoo, ya ce gidajen shugabannin kasa a Afirka ta kudu suna daga cikin muhimman wurare na gwamnati. Kuma akwai doka a kansu, saboda haka duk wanda ya dauki hotunsu, ya saba wa wannan dokar.

Karin bayani