Sarkakiya a shari'ar Bradley Manning

Bradley Manning Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bradley Manning

Hafsan sojan da ke jagorancin shari'ar da ake wa wani sojan Amirka da ake zargi da tsegunta bayyanan sirri ga shafin internet na Wikileaks, yayi watsi da bukatar da lauyoyin da ke kare sojan suka gabatar, ta yayi murabus.

Lauyoyin sun ce ne, ya kamata Hafsan sojin ya yi murabus, saboda yana nuna son kai a shari'ar.

Wakiliyar BBC ta ce, daya daga cikin lauyoyin da ke kare Bradley Manning, watau David Combs, ya yi zargin cewa Hafsan sojan ba zai yiwa Manning adalci ba, saboda yanzu yana aiki ne da ma'aikatar sharia ta Amirka, wadda yanzu haka take gudanar da bincike a kan Julian Assange, mutumen da ya kirkiro shafin na Wikileaks.

Bradley Manning ya bayyana ne a zaman farko na sauraren shari'ar da ake yi a Washington.

Wannan ne karon farko da yake fitowa a bainar jama'a tun bayan da aka kama shi a bara.

Private Manning dai yana fuskantar tuhumce-tuhumcen da suka hada da taimakawa abokan gaba.

Karin bayani