Rasha ta shammaci Kasashen yammacin duniya

Firayim Ministan Rasha Vladimir Putin Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rasha ta rarraba daftarin shawarwarin warware rikicin Kasar Syria

Rasha ta baiwa Kasashen yammacin duniya mamaki a taron majalisar dinkin duniya a New York ta hanyar rarraba wani daftarin da zai kawo karshen tashin hankali a Syria.

Gwamnatocin Kasashen yammaci sun shafe wata da watanni suna kokarin ganin majalisar tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da daftarinsu amma kuma Rasha da China sun hau kujerar naki.

Jami'an diflomasiyar Turai da Amurka sun yi maraba da daftarin na Rasha,amma sun yi korafi akan cewar daftarin baiyi bayanai sosai ba akan cin zarafin bil-adama da gwamnatin Syria ta yi .

Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vitaly Churkin yace an tsara daftarin shawarwarin ne da nufin kawo karshen tashe-tashen hankula a Syrian.

Karin bayani