Wata tawagar shiga tsakani daga Iraqi na Syria

Wata tawagar sasantawa daga Iraqi ta ta fi Syria don yin kira da a kawo karshen rikicin siyasar kasar. Tawagar wadda, mai baiwa gwamnatin Iraqin shawara ta fuskar tsaro, ya jagoranta, ta ce ta yi tattaunawa mai amfani da shugaba Bashar Al-assad.

Tawagar ta kuma ce hakazalika, ta ce ta tuntubi masu adawa da shugaban Syriyar.

'Yan Iraqin na kokarin cimma matsaya ne kan shawarwarin zaman lafiyar da kungiyar kasashen Larabaw ta bayar. Wakilin BBC ya ce 'yan Iraqin na tunanin suna da goyan bayan Amurka a yunkurin da suke yi, kuma suna da goyan bayan Iran ma.

Karin bayani