Amurka ta kammala kwashe sojojinta a Iraqi

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Amura ta kammala kwashe dakarun ta a Iraqi.

Hakan ya kawo karshen mamaye kasar shekaru taran da suka wuce, inda aka kawadda Saddam Hussein. Da sanyin safiyar Lahadinnan ne kimanin jerin gwanon motoci dari dauke da sojoji dari biyar suka tsallaka kan iyakar kasar zuwa Kuawait.

Dakarun Amurka dubu dari da saba'in ne suka kasance a Iraqin a kolacin a sansanoni fiye da dari biyar. Masu aiko da rahotanni sun ce yayin da wasu 'yan Iraqin ke murna da janyewar dakarun Amurkar, har yanzu wasu da dama na nuna damuwa ne game da yanayin tsaron cikin gida da kuma rikicin siyasar kasar.

Karin bayani