Kotun Kolin Congo ta tabbatar da zaben Mr. Kabila

Shugaba Joseph Kabila na Congo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kotun Kolin Congo ta tabbatar da zaben Joseph Kabila

Kotun kolin jamhuriyar demokradiyar Congo ta tabbatar da Joseph Kabila a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban Kasar da ake takaddama akai.

Kotun ta yi watsi da bukatar 'yan adawa na soke zaben.

A farkon wannan makon ne, Mr. Kabilla ya amince akan cewar an samu kura-kurai a wajen gudanar da zaben.

Kotun kolin a zamanta cikin kasa da awa guda a daren Juma'a, ta amince da sakamakon zaben da hukumar zabe ta fitar a makon daya gabata.

Karin bayani