Mutane ukku sun hallaka a wata fashewa a Najeriya

Hakkin mallakar hoto Reuters

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno ta Najeriya sun ce mutane ukku sun hakala a yayin da wani bam ya fashe a unguwar Shuwari two ta birnin.

Ganau dai sun tabbar da cewa karar ta razana wasu sassa na birnin inda mutane suka yi ta gudu don tsira da rayukansu.

Rundunar Hadin Gwiwar Samar da Tsaro a jihar - JTF - ta tabbatar da abkuwar lamarin.

Boko Haram ta ce 'yan kungiyar ta ne suka halaka a lamarin, kuma ta bayyana su da cewa shahidai ne

Hari a Kano

Wasu mutane da ba a kai ga tantance ko su waye ba, sun je unguwar Tudun Fulani a cikin unguwar Darmanawa dake birnin Kano inda su ka kashe kimanin mutane huddu ciki har da wani dan Acaba da kuma wani mai mota da suka yi awon gaba da motarsa bayan sun kashe shi.

Wasu da suka ganewa idonsu abun da ya faru, sun shaida wa BBC cewa, maharan sanye da dogayen riguna sun shafe sama da mintuna talatin suna harbe-harbe.

Bayanai dai sun ce banda kashe mutanen ba su dauki komai na dukiya ba.

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai ta ce sai nan gaba za ta yi karin bayani kan lamarin amma i zuwa yanzu suna zargin 'yan fashi ne.

Kalubalen tsaro

Najeriya dai na fama da tashe-tashen hankula.

Kungiyar Boko Haram ta sha daukan alhakin kai hare-haren da suka hada da tada bam a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da kuma babban ofishin rundunar 'yan sandan kasar dake Abuja a watannin baya.

Karin bayani