Wani jirgin ruwa ya nutse cikin teku a Indonesia

Jirgin Ruwa a Indonesia Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani jirgin ruwa ya nutse a tekun Indonesia

Masu ceto a Kasar Indonesia na cigaba da neman daruruwan mutanen da suka bace, bayan da wani jirgin ruwa ya nutse a kusa da tsibirin Java.

Jirgin na katako na kan hanyarsa ne zuwa Australia, inda yake dauke da baki daga Kasashen Afghanistan da Turkiyya da kuma Iran.

Wani jami'in 'yan sanda a yankin mai suna Totok Suharyanto ya ce akalla mutane 380 ne a cikin jirgin, amma kuma mutane 76 ne kawai aka iya cetowa.

Ya kuma kara da cewar jirgin ya kife ne sakamakon igiyar ruwa mai karfi, lamarin da ya sa fasinjojin suka fada cikin teku.

Wasu daga cikin su kuma sun yi ta iyo a cikin tekun har na fiye da sa'oi shida kafin masunta su gansu, su taimaka musu.

Karin bayani