An gano yunkurin kona majalisa a Masar

masu zanga zanga a Masar Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption masu zanga zanga a Masar

Majalisar Sojin dake tafiyar da mulki a Kasar Masar ta zargi masu zanga zanga a birnin Alkhahira da wani yunkuri na kokarin bankawa ginin majalisar dokokin kasar wuta.

A wani taron manema labarai, Janar Adel Emara, ya ce masu zanga zangar suna kokarin tsokanar sojoji yadda za a yi fito na fito a dandalin na Tahrir da kuma kewayensa.

Ya ce masu zanga-zangar suna tayar da zaune tsaye, tare da kuma kokarin hambarar da gwamnati.

Tun farko, an hallaka daya daga cikin masu zanga-zangar a wani dauki ba dadi da aka yi tare da ma'aikatan tsaro.

Jimlar mutane goma sha daya ne kawo yanzu suka rasa rayukansu a fito na fiton baya-bayan nan tsakanin bangarorin biyu, da aka fara ranar Juma'a.

Karin bayani