Wasu abubuwa sun fashe a Damaturu da Kaduna

Wasu abubuwa sun fashe a Damaturu da Kaduna
Image caption Wasu abubuwa sun fashe a Damaturu da Kaduna

Rahotanni daga Damaturu babban birnin jahar Yobe a arewacin Nageriya na cewa wasu abubuwa da ake zaton na hada bam ne sun fashe a wani gida a unguwar Ponpamari.

An ce daya daga cikin mutane ukkun da ke kokarin hada bam din ya jikkata, sannan sauran biyun sun tsere.

Rundunar 'yan sandan jahar Yoben ta ce suna ci gaba da neman mutanan biyu da suka tere. A wani labarin kuma rundunar 'yan sandan jahar Kaduna ta tabbatar da cewar wani abu ya fashe a wani kauye da ake kira Malkali Mando Akpata.

Rundunar yan sanda ta ce, bomb ne ake shirin hadawa a lokacin da ya fashe, kuma ya rutsa da mutane ukku.

Kawo yanzu babu cikakken bayani akan halin da wadannna mutane ke ciki.

Karin bayani