Kim Jong Un shi ne zai gaji mahaifinsa

Kim Jong Un Hakkin mallakar hoto AFP PHOTO KCNA VIA KNS
Image caption Kim Jong Un

Kasar Koriya ta arewa ta yi kira ga al'ummarta da su marawa dan tsohon shugaban kasar Kim Jon ill baya a matsayin sabon shugaba, bayan sanarwar rasuwar tsohon jagoran kasar.

Gidan talabijin na kasar ya sanar da sunan Kim Jong Un, wanda bai kai shekaru talatin da haihuwa ba a matsayin magajin gwarzon shugaban kasar.

Mutane da dama a kan titunan Pyongyang babban birnin kasar ta Koriya ta arewa sun yi ta rusa kuka.

Kamfanin dillancin labaran kasar ya ce tsohon shugaban ya rasu ne sakamakon bugun zuciya a lokacin da yake tafiya a cikin jirgin kasa a ranar Asabar din da ta gabata.

Karin bayani