Syria ta yadda masu sa ido su je kasar

Masu zanga zanga a Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga zanga a Syria

Syria ta amince ta kyale masu sanya ido na kungiyar kasashen larabawa su shiga kasar ta, a matsayin wani bangare na kokarin kawo karshen amfani da karfi wajen murkushe masu zanga-zanaga da ke adawa da gwamnati.

A wani jawabi da aka watsa ta gidan talabijin na kasar, Ministan harkokin wajen kasar Walid al-Muallem, ya ce an sanya hannu a kan yarjejeniyar bayan kungiyar kasashen larabawan sun amince da wasu gyare-gyare da Syria ta nemi a yi.

To amma har yanzu babu karin haske game da wannan yarjajeniyar da Syrian ta sawa hannu.

Fiye da mutane dubu biyar ne aka kashe, a zanga zangar da aka kwashe watanni tara ana yi a Syriar.

Karin bayani