Takaddama tsakanin gwamnatin Filato da al'ummar Hausawa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

A jihar Filaton Nijeriya wata sabuwar takaddama ta kunno kai tsakanin gwamnatin jihar da kuma al'ummar hausawa inda hausawan ke zargin gwamnatin da maida su saniyar ware wajen gudanmar da ayyukan raya kasa kamar hanyoyin mota da gina asibitoci da makarantu da ruwan sha da makamantansu, duk da cewa a cikin babban birnin jihar suke. To sai dai kuma gwmnatin jihar ta Filato ta bayyana cewa ba wai bata son gudanar da ayyukan ba ne a yankunn hausawa, rashin cikaken tsaro ga 'yan kwangila a yankunan na hausawan ne ke hana gudanar masu da ayyukan raya kasar, kuma da zarar cikakken zaman lafiya ya samu a karamar hukumar Jos ta arewa inda husawan suka fi rinjaye, to gwamnatin za ta aiwatar da ayyuka a yankin. An dai dade ana fama da rigingimu masu nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa a jihar ta Filato inda akan samu asarar rayuka da dukiya. Dama dai a sakamakon yawan tashe-tashen hankula da ake yawan fuskanta jihar ta Filato, al'umar Hausawan na Jos suka shiga kallon hadarin kaji da gwamnatin jihar Jonah Jang, inda al'ummar husawan ke korafin cewa gwamnatin ba ta yi musu adalci. Hatta ga irin 'yan ayyukan raya kasa da gwamnatin ke gudanarwa a jihar, al'umar husawan na birnin jos sun bayyana cewa basa gani a yankunansu duk da cewa a cikin babban birnin jihar suke. To sai dai kuma a cewar gwamna Jonah Jang, matsalar tsaro ce ta ke hana gudanar da ayyuka a yankunan husawan, kuma zancen nuna wariya daga gwamnatinsa ba gaskiya ba ne. To sai dai kuma cewar shugaban kungiyar Jasawa wato Husawan Jos, Alhaji 'Shehu Ibrahim Msalla, babu ko kishin gaskiya a ikirarin na gwamnan jihar Filato, domin hasali ma da gangan gwamnatin tasa ta maida su saniyar ware, kuma suna irin rayunan ce ta garin dadi na nesa. Sai dai duk da irin wanann takaddama da ake yi a tsakanin gwamnatin jihar ta Filato da kuma al'ummar husawan, gwamnan na jihar Filato, yayin da yake gabatar da kasafin kudi na shekra ta dubu biyu da goma sha biyu ga majalisar dokokin jihar ya nunar da cewa zai rungumi kowa da kowa, alkawarin da aka zuba masa ido domin ganin ko zai cika.