Makomar Iraqi bayan janyewar Amurka daga kasar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nour al-maliki

A makon jiya ne Amurka ta janye sojojinta daga kasar Iraqi bayan da ta kwashe kusan shekaru goma a kasar.

Amurka dai ta shiga kasar ce a shekarar 2003 lokacin da ita da kawayenta suka yi zargin cewa tsohon shugaban Iraqi, Saddam Hussaini, na shirin kera makaman nukiliya, zargin da ya sha musantawa.

Yakin na Iraqi ya haddasa mutuwar dubban jama'a, kuma ya lashe makudan kudade.

Dakarun sojin Amurkan dubu dari da saba'in ne suka kasance a Iraqin a lokacin da kuma sansanoni sama da dari biyar.

Tun bayan tumbuke marigayi Saddam Hussein dai kasar ta Iraqi ta yi ta fama da tashen-tashen hankula wadanda ke hallaka jama'a.

Shugaban Amurka, Barack Obama, ya yi godiya ga dukkanin wadanda suka yi aiki a Iraqi, ya kuma ce sun bar kasar cikin kwanciyar hankali da yanci, duk da cewa ba komai ne ya daidaita ba.

Tsugune-bata-kare ba

Sai dai masu-fashin baki akan harkokin kasar na cewa janyewar Amurka daga Iraqi ba za ta kawo zaman lafiya a kasar ba.

Malam Aminu Daurawa, wani masanin harkokin Gabas Ta Tsakiya ne, ya shaidawa BBC cewa Amurka ta dora 'yan barandarta akan mulkin kasar, don haka da wuya a samu zaman lafiya.

Tsakanin 'yan Shi'a da 'yan Sunnah

Ficewar Amurka daga Iraqi ke da wuya sai tsohuwar gabar da ke tsakanin 'yan Shi'a da 'yan Sunnah da ke mulkin kasar ta kunno kai.

Babbar jam'iyyar adawa a kasar ta fice daga zauran majalisar dokokin kasar domin nuna kin amincewarta da abin da ta kira kaka-gidan da Firayim Minista, Nouri al-Maliki, ke yi wajen yanke shawara kan al'amuran kasa.

Mataimakin Pirayim Ministan kasar, dan Sunni, Saleh Al Mutlaq, ya ce kasar na kasadar afkawa cikin wani sabon rikicin addini saboda matakan da Mr Al-Maliki, wadan ke bin darikar Shi'a ke dauka.

Saleh Al - Mutlaq ya zargi Maliki da kasancewa wanda ya fi Saddam Hussein bakin mulki.

A bangarensa, Mr Al-maliki ya ce bashi da niyyar kawo fitina a kasar.

Wani Kakakinsa ya bukaci dukkanin bangarorin da su yi tattaunawa don warware matsalar.

Wannan cece-kuce da ake yi a kasar ta Iraqi dai, ya sanya masu sharhi game da kasar na cewa, ba zai haifa mata da-mai-ido ba.

Karin bayani