Sama da mutane 1000 sun mutu a Philippines

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ambaliyar ruwa ta yi kaca kaca da gidaje a kudancin Philippinnes

Ruwa da iska da suka haddasa ambaliyar da ta yi kacakaca da kudancin Philippines sun yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan dubu daya, yayinda har yanzu ba a san inda daruruwa su ke ba.

Jami'ai a garuwa biyun da abin ya shafa a tsibirin Mindanao, inda ruwa ya tafi da mutane suna barci a wasu unguwannin marasa galihu da ke kusa da gabar teku, na ta fama da gawarwakin ba su kwashe ba.

Jami'an sun ce lallai ne a suturta gawarwakin.

Shugaba Benigno Aquino na ziyara a yankin don ganin irin barnar da ta auku.

Wakiliyar BBC ta ce an zargi gwamnati da rashin shiri yadda ya kamata don tunkarar ruwan da iska mai tsanani, da kuma rashin katabus wajen tunkarar abin da ya biyo baya.