Kungiyoyin siyasa sun yi Allah wadai da Isra'ila

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zauren kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya

A wani mataki da ba a saba ganin irinsa ba, dukkan kungiyoyin siyasar da ke da wakilici a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, sun hadu wajen yin Allah wadai da matakan da Isra'ila ke dauka na gina sabbin matsugunan Yahudawa a yankunan Palasdinawa.

Wakilan kasashen sun yi gargadin cewa ci gaba da gina matsugunan na baraza ga yiwuwar samun kasar Falasdinu, sannan suka nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da samun tashin hankali a yankunan 'yan kama wuri zauna.

Bayan jawabin wakilin Majalisar Dinkin Duniya a yankin Gabas ta Tsakiya, wakilan kasashe da dama sun fito wajen kwamitin sulhu inda suka yi Allah wadai da ci gaba da gina matsugunen yahuduwa da Isra'ila ke yi.

Kungiyoyin sun hada da wakilan Tarayyar Turai da na Non Aligned Movement, da na kasashen Larabawa, da na kasashe masu tasowa da ake wa lakabi IBSA, da kuma Rasha.

Halin da ake ci a yunkurin samar da zaman lafiya a yankin ne ya sanya su ikirarin cewa, halayyar Isra'ila na barazana ne ga komawa tattaunawar zaman lafiya ba.

Sannan suka nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da kai hare-hare kan Palasdinawa a yankunan 'yan kama wuri zauna.

Ambassadan Burtaniya Mark Lyall Grant wanda ya yi magana a madadin Tarayyar Turai ya ce; "mun yi imani cewa tsaron Isra'ila da samun kasar Palasdinu ba abubuwa bane da cin karo da juna.

"A maimakon haka suna ma karfafa juna ne.

"Amma ba za su samu ba idan ana ci gaba da gina matsugunen Yahudawa da kuma kaiwa Palasdinawa hare-hare."

Duk da yawan jami'an da suka yi magana, ba su iya kai ga samar da wani jawabi a hukumance daga Kwamitin sulhun ba, saboda sun san Amurka za ta hau kujerar naki.

A matasayinta na kawar Isra'ila, Amurka na ganin duk wani yunkurin samar da zaman lafiya kamata yayi ya zo a karkashinta bawai Majalisar Dinkin Duniya ba.

Amma wasu mambobin kwamitin na ganin lokaci ya yi da kwamitin ya kamata ya kara kutsa kai cikin lamarin, ganin yadda al'amura ke kara tabarbarewa ta fuskar diflomasiyya da kuma tsaro.