Koriya ta Arewa: Amurka na neman sauyi cikin lumana

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Shugaba Obama ya jaddada alkawarin Amurka na kasancewa tare da kawayenta da ke yankin gabashin Asiya, bayan rasuwar jagoran Korea ta Arewa, Kim Jong il.

Tun da farko dai Amurka da Japan sun yi kira da a tabbatar an yi sauyin shugabanci cikin lumana a kasar ta Korea ta Arewa.

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton, ta ce kasashen biyu na da muradi iri daya na ganin an samu sauyin shugabanci cikin lumana da kwanciyar hankali a Korea ta Arewa da kuma tabbatar da zaman lafiya da lumana a yankin.

Wani kakakin fadar White House ya ce Amurka na fata Korea ta Arewa za ta sauke nauyin da rataya a wuyanta na kawo karshen shirinta na kera makaman nukiliya.

Kim Jong-il ya mutu ranar Asabar

Kim Jong-il ya rasu a ranar Asabar sanadiyar ciwon zuciya. Gidan talbijin din kasar ya bayyana mutuwarsa da safiyar ranar Litinin. Kim Jong-il dai na shirin yadda dansa na uku ne, Kim Jong-un zai gajeshi kafin ya rasu.

Rashin kammala shirin yadda dansa zai gaje shi ne yasa masu sharhi a kan al'amuran yankin ke ganin kasar za ta shiga cikin halin rashin tabbas ganin yadda take tafiyar da al'umaranta ita kadai, duk da cewa tana da makaman nukiliya.

Kasar Koriya ta arewa ta yi kira ga al'ummarta da su marawa dan tsohon shugaban kasar Kim Jong-il baya a matsayin sabon shugaba, bayan sanarwar rasuwar tsohon jagoran kasar.

Gidan talabijin na kasar ya sanar da sunan Kim Jong Un, wanda bai kai shekaru talatin da haihuwa ba a matsayin magajin gwarzon shugaban kasar.

Mutane da dama a kan titunan Pyongyang babban birnin kasar Koriya ta arewa sun yi ta rusa kuka.

Kamfanin dillancin labarai na Yonhap ya ruwaito cewa sakataren tsaron Amurka da na koriya ta kudu sun tattauna ta wayar tarho inda suka amince kan su hada kai wajen sanya ido a al'amuran da ke tafiya a kasar Koriya ta arewa yayin da za su sanya sojojinsu a shirin ko-ta-kwana.

Karin bayani