Mataimakin Shugaban kasar Iraqi ya zargi Fira Minista

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mataimakin Shugaban kasar Iraq, Tariq al-Hashemi

Mataimakin Shugaban kasar Iraqi, Tariq al-Hashemi ya zargi Fira Ministan kasar, Nouri al-Maliki da rura wuta rikici a kasar bayan ya bada sammacin kame shi.

Mista Hashemi ya shaidawa BBC cewa Mista Maliki ya fara wani abun ne da ya kasa shawa kanshi abun da kuma yasa al'ummar Iraqi su ka nuna damuwa a kai.

Ana dai zargin Mista Hashemi ne da kitsa ta'adanci, kuma a yanzu haka yana yankin kwardawa mai kwarya kwaryar cin gashin kansa a Iraqin.

Mutane da da dama ne su ka mutu a kasar bayan da wasu bama-bamai su ka tashi a kasar a jiya alhamis.

Hashemi, wanda Maliki ya bada sammacin kame shi, ya ce dolene a daurawa Pira Ministan kasar laifin tashin hankalin da ake samu a kasar saboda ya bar al'ummuran tsaro ya maida hankali wajen murkushe 'yan adawa.

Fargaba

Akwai fargabar cewa dai sabon tashin hankalin da ya barke a kasar na iya haddasa yankin basasa a kasar.

Mista Maliki dai ya fito ne da bangaren 'yan shi'a mafi rinjaye a yayinda Mista Hashemi dan siyasa na bangaren Sunni ne da ake ji da shi.

Ana dai zargin Hashemi ne da kitsa hare haren ta'adanci a kan jami'an gwamnati da kuma jami'an tsaro abun da kuma ya musanta.

Tunni dai gungun jam'iyyar 'yan Sunni su ka kauracewa Majalisar dokokin kasar da kuma gwamnatin, yayinda ake ci gaba da zaman dar dar a gwamnati.

Mista Hashemi a baya dai ya kwantata hallayar Pira Ministan kasar da na tsohon Shugaban kasar, Marigayi Saddam Hussein.

Hare haren da aka kaddamar a kasar a jiya alhamis, shine mafi muni a 'yan watannin nan, kuma ya zo bayan da Amurka ta janye dakarun ta a kasar bayan kusan shekaru tara.

Karin bayani