Gilani ya soki sojojin Pakistan

Yousuf Raza Gilani Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yousuf Raza Gilani

Praministan Pakistan, Yusuf Reza Gilani, ya yi kakkausar sukar da bai taba yin irinta ba akan rundunar sojin kasar, wadda ke da tasirin gaske akan harkokin siyasar kasar.

Mista Gilani ya ce bai kamata rundunar sojin kasar ta nuna cewa kamar tafi karfin doka ba, kuma dole ne ta rika yi wa majalisar dokokin kasar biyayya.

Praministan ya ce, ya na jin akwai makarkashiyar neman hambarar da gwamntinsa, sai dai bai danganta makarkashiyar da sojin kasar ba.

Yusuf Reza Gilani yayi kalaman ne, bayan da wasu takardun da aka fallasa ke nuna cewa, ana neman Amirka ta taimaka wajen hana wani juyin mulki a Pakistan.

Karin bayani