Ana ta kokarin hada kan bangarorin Palasdinawa

Palasdinawa Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Palasdinawa

Bangaran Palasdinawa na Hamas da ke iko a Gaza--- zai shiga kungiyar Palastine Liberation Organisation.

Hamas ta cimma yarjejeniyar zama mamba ta kungiyar PLO din da abokiyar gabarta ta Fatah wadda ke da iko a gabar yammacin kogin Jordan.

Wakiliyar BBC a yankin gabas ta tsakiya, ta ce yarjejeniyar wadda ta biyo bayan tattaunawar da aka kwashe kwanaki uku ana yi a birnin Alkahira, wani ci gaba ne wajan sasanta Palasdinawan.

Sai dai kuma ta ce ba makawa shigar Hamas kungiyar zai dagula batun samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya, saboda Hamas bata yadda da tattaunawa da Isra'ila ba, wadda kungiyar PLO din ke yi shekaru ashirin din da suka wuce.

Karin bayani