Tshisekedi na shirin rantsar da kansa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jagoran 'yan adawa Etienne Tshisekedi

A yau alhamis ne ake sa-ran jagoran 'yan adawar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, Etienne Tshisekedi, zai yi kokarin rantsar da kansa a matsayin shugaban kasa.

Jagoran 'yan adawan zai rantsar da kanshi ne, duk da cewa kotun kolin kasar da ma Hukumar zabe sun tabbatar da cewa Shugaba Joseph Kabila ne ya lashe zaben da gagaruminn rinjaye - wanda kuma tuni aka rantsar da shi.

An dai girke jami'an tsaro da tankoki a wajen filin wasa na birnin Kinshasa inda Mr Tshisekedi ke shirin yin bikin rantsuwar ta sa.

Takardun gayyatar da aka rarraba sun yi kama ne da takardu ne na hukuma.

Shugaban 'yan adawan dai ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar, a yayinda ya yi aiyana kanshi a matsayin wanda ya yi nasara.

Masu sa ido na cikin gida da kuma kasashen waje sun ce an tafka kurakurai a zaben a yayinda su ke nuna tababa game da sakamakon.

Jami'an diplomasiyya dai sun nemi da a sasanta, amma mutane da dama sun rasa rayukansu a rikicin da ya biyo bayan zabe a Kinshasa da kuma inda 'yan adawa ke da tasiri.

Karin bayani