An tarar Chevron a Brazil saboda malalar mai

cehrobn Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Malalar mai a tekun Brazil

Cibiyar kula da muhalli ta kasar Brazil ta ci tarar kamfanin man Amurka Chevron, fiye da dala miliyon biyar saboda saba ka'idar lasisin muhalli akan yadda kamfanin yayi aikin malalar mai a watan Nuwamba.

Cibiyar muhallin mai suna Ibama ta ce Chevron baida na'urorin da suka dace, kuma ya bata lokacin wajen aikin bayan da wasu bututan mai suka fashe.

A baya dai cibiyar taci tarar Chevron dala miliyon 28 akan abubuwan da suka shafi malalar mai.

Daya daga cikin rijiyoyin man Chevron ya malalar da mai akalla gangan dubu uku a kusada gabar tekun Brazil.

Masu shigar da kara na gwamnati sun gabatar da lamarin gaban kuliya suna bukatar kotu ta dakatar da Chevron daga gudanar da ayyuka a Brazil da kuma bukatar makudan kudade daga wajen kamfanin akan illar da ya yiwa muhalli.

Karin bayani