Tshisekedi ya rantsar da kansa Shugaban Congo

Jjagoran 'yan adawa Etienne Tshisekedi na Congo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jjagoran 'yan adawa Etienne Tshisekedi na Congo

Jagoran Yan adawa na Congo, Etienne Tshisekedi, ya rantsar da kansa a matsayin Shugaban kasa a wani buki a gidansa a Kinshasa babban birnin kasar.

An hana wa magoya bayansa kaddamar da shi Shugaban kasa a Babban filin wasa, wanda yansanda da soji dauke da makamai suka yiwa kawanya.

Yansanda sun haramta wani taron gangami na yan adawa sannan sun yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa magoya bayan yan adawa.

An kuma kama mutane da yawa, aka dauke su zuwa Ofis Yansanda ko kuma sansanonin soji.

A ranar talata ne dai aka rantsar da Shugaba Joseph Kabila, amma kuma masu sa ido na kasashen waje sun ce an tabka munanan kura -kurai a zaben.

Karin bayani