Hankali ya fara kwantawa a garin Damaturu na Najeriya

Yansanda a Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yansanda a Najeriya

Rohotanni daga Najeriya na cewa an fara samun kwanciyar hankali a garin Damaturu babban birnin Jihar Yobe a arewacin kasar bayan musayar wutar da jami'an tsaro suka yi ta yi da wasu 'yan bindida.

Yanzu dai jami'an tsaro na sintiri a garin na Damaturu bayan artabun da suka shafe yinin yau suna yi da wadanda ake zargin yan kungiyar nan ce ta Jama'atul Ahlus Sunna Lil-Da'awati wal Jihad, wadda aka fi sai da Boko Haram.

Kwamishinan 'yan sandan Jihar Yoben ya ce an kashe mutanen da ake zargin 'yan Boko Haram ne su goma sha biyu da jami'an 'yan sanda biyu a lokacin musayar wutar, baya ga wadanda aka kama.

Jami'an tsaro sun umarci mazauna wasu unguwanni a Damaturu da su fice dazu daga gidajen su lokacinda aka tura karin jami'an tsaro don tunkarar 'yan bindigar.

Sai dai wasu mazauna garin sun ce tuni har sun fara komawa gidajensu.

Tun a jiya ne dai aka fara jin karar harbe harbe da fashewar bama bamai a garuruwan Potiskum da Damaturun dama Maiduguri babban birnin Jihar Borno mai makwabtaka da Yoben

Karin bayani