Matsalar karancin cimaka a Nijer

nijet Hakkin mallakar hoto b
Image caption Matsalar cimaka a jamhuriyar Nijer

Bisa dukkan alamu dai, matsalar karancin abinci tana neman zama ruwan dare a Jumhuriyar Nijar inda kusan kowacce shekara ake fuskanta irin wannan matsala a wasu yankunan kasar.

Ko a kwanan baya, sai da wasu kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da kungiyar agaji ta Oxfam, suka yi gargadin cewa kasashen yankin Sahel za su iya fuskantar matsalar yunwa a shekara mai zuwa, muddin gwamnatocinsu ba su dauki kwararan matakai tun yanzu ba.

A cewar wani rahoton na hukumar abinci ta duniya, WFP ko PAM, kimanin 'yan Nijar miliyan daya ne za su fuskanci mummunan karancin abinci a badin. Sai dai tuni gwamnatin kasar ta ce ta ware kusan CFA billiyan 21 don magance wannan matsala.

Karin bayani