Babban Hafsan Sojin Pakistan ya kawar da yiwuwar juyin mulki a kasar

Pirayim Minista Raza Gilani na Pakistan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Pirayim Minista Raza Gilani na Pakistan

Babban hafsan mayakan kasa na Pakistan, Janar Ashfaq Kayani, ya kawar da batun cewa sojoji za su yi juyin mulki a Pakistan.

Janar Ashfar Kayani ya ce duk wata jita-jitar scewar soji na hirin kwace mulki ba gaskiya ba ne.

A wani jawabi da yaiwa majalisar dokikin kasar ta Pakistan ranar alhamis,Pirayim Minista, Yusuf Raza Gilani, ya yi gargadi kan wani shirin kifarda zababbiyar gwamnatin kasar.

Sai dai kuma a martanin da ya mayar, janar Kayani ya ce irin wannan na dauke hankali ne daga ainahin abubuwan dake faruwa.

Karin bayani