'Yan adawa sun ce gwamnati ce ta kitsa kunar bakin waken Syria

Hakkin mallakar hoto AP

'Yan adawa a Syria sun ce hukumomin kasar ne suka shirya harin kunar bakin waken kasar da ya yi ajalin mutane arba'in a babban birnin kasar Damascus

'Yan adawan sun ce gwamnatin kasar na son ta nuna wa tawagar kungiyar kasashen larabawa cewa ai masu tada kayar baya nada karfi a kasar.

Jami'an gwamnatin Syria sun ce wasu 'yan kunar bakin wake a cikin motoci biyu sun kashe mutane fiye da arba'in a wasu hare hare da aka kai wa hukumomin tsaro a Damascus babban birnin kasar.

An nuna hotunan ma'aikatan ceto na ta kwashe buraguzai daga hedikwatar ma'aikatar tsaro; inda aka kaiwa wani gini dake kusa da wajen harin shima.

Gidan talabijin din kasar ta Syria ya ce binciken farko ya gano hannun kungiyar al -qaeda a harin.

Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen Syria, Jihad Macdashee ya shaidawa BBC cewa kwanaki biyun da suka wuce sun samu gargadi daga Labanon, amma zai yi wuya ka kare kai irin wadannan hare haran.

Karin bayani