Ana neman tuhumar wasu 'yan majalisa a Niger

Taswirar Niger
Image caption Taswirar Niger

A jamhuriyar nijar gwamnati ta dau matakin aika ma majalisar dokoki sunayen wasu yan majalisar su 8 da take zargi da hannu a almundahna domin cire musu rigar kariya, ta yadda za su iya fuskantar shari'a.

Wadannan yan majalisar dai duk da cewa gwamnatin ba ta bayyana sunayensu ba,sun hada da na bangaren adawa da bangaren masu mulki.

A ranar lahadi ne ministan shari'a kuma kakakin gwamnatin Niger din, Malam Maru Amadu zai aika ma majalisar sunayen nasu.

Dazu da yamma ne Ministan shari'ar ya tabbatar da hakan a wajen wani taron manema labarai da ya kira a Yamai.

Karin bayani