Ana kara sa matsin lamba akan fadar Kremli

Masu zanga zanga a Moscow Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zanga a Moscow

Dubban masu zanga zanga sun taru a Moscow babban birnin kasar Rasha, a zanga zangar baya bayannan kan kin amincewa da zabukan majalisar dokokin da akai a wannan watan.

Tsohon ministan kudin Rasha, Alexei Kudrin ya fadawa masu zanga zangar cewa an tabka magudi kuma akwai bukatar a sake yin wasu zabuka da sabbin dokokin zabe.

Ya ce ya yadda da babban batun da ake na cewa an murda zaban, dan haka ne ya ke san aikewa mahukunta sako cewa a gudanar da bincike a kuma hukunta duk wanda aka kama da hannu a cuwa-cuwar da aka yi a lokacin zaban.

Sakamakon da aka bayyana dai ya ba jam'iyyar praministan Vladimir Putin nasara.

Karin bayani