Ba Amurke mai shekaru 15 ya hau tsaunin vinson

romero
Image caption Jordan Romero da iyayensa

Wani matashin ba Amurke ya kasance mafi karancin shekaru a duniya daya hau kan tsaunukan da suka fi kowanne girma a duniya a cikin nahiyoyi bakwai daban daban.

Jordan Romero mai shekaru 15 ya hau tsaunin Vinson dake Antartica a ranar Asabar, wato bukatarsa ta karshe na abinda ya soma shekaru biyar da suka wuce.

Tawagar tasa data kunshi mahaifinsa da kishiyar mamansa, ana anasaran a yau Lahadi zasu sakko don komawa sansanninsu.

Wakiliyar BBC ta ce "Jordan da maihaifinsa sun ce suna hawan tsaunukan ne don su tsima matasa su zama masu kuzari don rage yawan samun matsalar kibar data wuce kima".

A matsayinsa na dan shekaru goma da haihuwa, Jordan Romero ya hau saman tsaunin Kilimanjaro dake nahiyar Afrika.

Yana kuma da shekaru goma sha a duniya, ya haye saman tsauni mafi girma a duniya wato tsaunin Everest.