Gwamnatin Najeriya ta yi tir da hare haran da aka kai

Harin bam a Madalla Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Harin bam a Madalla

Rahotanni daga Nigeria sunce mutane akalla talatin ne suka rasa rayukansu, bayan wasu jerin hare hare da aka kai a wasu Jihohin kasar.

Hari na farko, ya faru ne a wata Muja'mi'a da ke garin Madalla a Suleja da ke Jihar Naija mai makwabtaka da Abuja babban birnin Nigeriar, inda mutane akalla ashirin da biyar suka mutu yayin da wasu suka samu raunika.

Haka nan kuma wani dan kunar bakin wake ya kai hari a wani ofisihin jami'an tsaro a Damaturu, babban birin Jihar Yobe, yayin da a Jos kuma wani bomb ya fashe a kofar wani coci, inda aka ce dan sanda guda ya mutu.

Kungiyar nan ta Ahlus Sunna lid-da'awati wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram ta amsa cewar ita ta kai hare haren.

Tuni Gwamnatin Nigeria, ta yi Allah wadai da hare-hare, ta na mai nanata cewar, zaa zakulo wadanda suka kai su domin gurfanar da su a gaban shari'a.

Karin bayani