Tauraron Imran Khan na kara haskawa a Pakistan

'Yan siyasar Pakistan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan siyasar Pakistan

Magoya bayan tsohon dan wasan kurket din nan na kasar Pakistan, Imran Khan sun yi wani gangami a Karachi---- inda jam'iyyar dake mulki ta Pakistan Peoples' Party ke da karfi.

A 'yan watannin baya bayan nan Mr Khan wanda ke jagorantar jam'iyyar adawa ta Movement for Justice na ta samun goyan baya, kuma manyan 'yan siyasa da dama na ta komawa jam'iyyar tasa.

Wakilin BBC ya ce shiga birni mafi girma a Pakistan yanzu zaka ga hotunan Imran Khan ko ina.

Dubban mutane sun saurari jawabinsa da yai tir da cin hanci da rashawa a siyasar Pakistan, wanda yai a watan Oktoban da ya gabata.

Karin bayani