Fadar Vatican ta yi tir da hare haran bam a Najeriya

Fadar Vatican Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Fadar Vatican

Fadar Vatican ta yi allawadai da tashin bam din da aka samu a Abuja da cewa abu ne mara ma'ana kuma ta'addanci ne da zai rura wutar gaba.

A jawabin da ya saba yi kowace ranar kirsimeti a dandalin St Peter dake fadar Vatican, Paparoma Benedict ya yi kiran da a kawo karshen zub da jini a Syria da kuma sake komawa ga tattaunawar zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

Paparoma ya ce yana fatan tashe tashen hankulan da ake a kasashen larabawa zai haifar da kyakykyawan sakamako.

Har ila yau Paparoma ya yi kira ga kasashen duniya da su taimakawa mutanan dake fama da yunwa a kusurwar kudu da hamada.

Karin bayani